Acts 4

Bitrus da Yohanna a Gaban Majalisa

1Sai firistoci da shugaban masu gadin haikalin da kuma Sadukiyawa suka hauro wurin Bitrus da Yohanna yayinda suke cikin magana da mutane. 2Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu. 3Sai suka kama Bitrus da Yohanna, amma da yake yamma ta riga ta yi sai suka sa su cikin kurkuku sai washegari. 4Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar.

5Washegari, sai masu mulki, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru a Urushalima. 6Annas babban firist yana nan, haka ma Kayifas Yohanna, Alekzanda da kuma sauran mutanen da suke iyalin babban firist. 7Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa: “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?”

8Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu: “Masu mulki da dattawan mutane! 9In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi, 10to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Israʼila cewa: Da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye. 11Shi ne,

“ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi,
wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’
Zab 118.22

12Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”

13Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu. 14Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi. 15Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, saʼan nan suka yi shawara da juna. 16Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba. 17Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”

18Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu. 19Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shariʼanta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah. 20Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”

21Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru. 22Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arbaʼin.

Adduʼar Masu Bi

23Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu. 24Saʼad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin adduʼa ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu. 25Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa:

“ ‘Don me ƙasashe suke fushi,
mutane kuma suke ƙulla shawara a banza?
26Sarakunan duniya sun ja dāgā,
masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya,
suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’
Zab 2.1, 2

27Hakika Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Alʼummai da kuma mutanen Israʼila a wannan birni ne don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe. 28Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru. 29Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali. 30Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”

31Bayan suka yi adduʼa, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka ciku da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.

Masu Bi Sun Raba Mallakarsu

32Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi. 33Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka. 34Babu mabukata a cikinsu. Lokaci lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar, 35su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.

36Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa) 37ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni.

Copyright information for HauSRK